Wata kotu a Ingila ta dage tsohon dan kwallon kulob din Manchester United da kuma kasar Ingila Wayne Rooney daga yin tuki har na tsawon shekara biyu.
Shi dai Rooney tun a ranar 1 ga watan Satumbar wannan shekara ce jami’an tsaron Ingila suka same shi da laifin yin tuki bayan ya bugu da giya da tsakar dare da hakan ya saba wa dokar yin tuki ta Ingila.
Hakan ce ta sa jami’an suka shigar da kara kotu, kuma a ranar Litinin da ta wuce ne kotun ta yanke masa hukunci na dage shi daga yin tuki a Ingila na tsawon shekara biyu, bayan bai yi gardamar aikata laifin yin tuki alhali ya bugu da giya ba. Yanzu dai Rooney bai isa ya tuka kowace irin mota a Ingila ba, har sai bayan shekara biyu.
Rahoton da kafar watsa labarai ta BBC ta kalato ya nuna yanzu dan kwallon direba ne ko matarsa ke kai shi unguwa ko filin kwallo a duk lokacin da zai fita daga gida.
Tuni dan kwallon da yanzu haka yake buga wa kulob din Eberton ya ba magoya bayansa hakuri a kan wannan abin kunya da ya yi, kuma ya sha alwashin hakan ba za ta sake aukuwa da shi nan gaba ba.