A shekaranjiya Laraba ne Kwamitin ladabtar da ’yan kwallo na hukumar shirya kwallo a Sifen (FA) ya bayar da sanarwar dakatar da dan kwallon FC Barcelona na Sifen Pikue daga yin wasanni hudu a gasar La-Liga da za a fara yau Juma’a.
Gerard Pikue dai kwamitin ya same shi ne da laifin zagin mataimakin alkalin wasa a ranar Litinin da ta wuce a lokacin da wasa ke gudana a tsakanin FC Barcelona da na Athletic Bilbao a wasa zagaye na biyu na cin kofin Spanish Super Cup. An tashi wasan ne da ci 1-1 sannan 5-1 idan aka hada wasannin biyu, al’amarin da ya sa Bilbao ta lashe kofin. Zagin da dan kwallon ya yi wa mataimakin alkalin wasa ne ta sa alkalin wasan ya ba shi katin kora (red card) ba tare da bata lokaci ba. Daga nan ne hukumar ta kafa kwamiti a kan dambarwar kuma ta same shi da laifi.
Kwamitin ya ce an dage dan kwallon daga wasanni hudu na gasar da hakan ya nuna ba zai buga wasan da kulob din zai yi da na Bilbao ba a jibi da kuma wanda kulob din zai yi da na Atletico Madrid a ranar 12 ga watan gobe da kuma wasannin da kulob din zai hadu da na Malaga da kuma na Lebante.
…An dage Pikue daga yin wasannin hudu
A shekaranjiya Laraba ne Kwamitin ladabtar da ’yan kwallo na hukumar shirya kwallo a Sifen (FA) ya bayar da sanarwar dakatar da dan kwallon FC…