✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dage dokar hana Sallar Juma’a a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta dage dokar hana Sallar Juma’a da zuwa coci ranar Lahadi da ta sanya a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus. Jami’in…

Gwamnatin Jihar Katsina ta dage dokar hana Sallar Juma’a da zuwa coci ranar Lahadi da ta sanya a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandar Jihar SP Gambo Isa ya ce gwamnatin jihar ta dage dokar ne tun daga karfe 6 na safe har zuwa karfe 7 na yamma a ranakun Juma’a da Lahadi.

SP Gambo ya bayyana wa ‘yan jarida a ranar Alhamis cewa hakan zai ba wa mabiya addinan biyu damar gudanar da ibadu a ranakun biyu masu muhimmanci a garesu.

Sai dai ya kara da cewa dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya tana nan ba a dage ta ba a sauran ranakun.

Sannan dokar takaita zurga-zurgan ababen hawa a kananan hukumomin da ba a rufe ba tana nan daram.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga Musulmai da Kiristocin Jihar su yi amfani da damar wurin ci gaba da yi wa Jihar addu’o’in samun zaman lafiya da yayewar annobar coronavirus.