An dage wani dan kwallo mai suna Isma’il Gunduz da ke buga kwallo a gasar rukunin ’yan dagaji (amateur) da ke kasar Austiriya bayan ya zagba wa alkalin wasa karo kuma ya tsaga masa lebe inda aka garzaya da alkalin wasan asibiti aka kwantar da shi don yi masa magani.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da wasa ke gudana a tsakanin kulob din Isma’il mai suna SK Rum da na SPG Innsbruck West a daidai minti na 86 a lokacin da alkalin wasan ya ba Isma’il katin gargadi na biyu (Yellow Card) kafin ya kara masa da jan kati (Red Card) inda nan take Isma’il ya nufi inda alkalin wasan yake kuma ya zagba masa karo da kai da hakan ta sa alkalin ya zube kasa warwas da fasasshen lebe.
Jim kadan da faruwar al’amarin ne hukumar shirya kwallon kafa ta kasar ta bayar da sanarwar dage dan kwallon har na tsawon wasanni 70 ba tare da bata lokaci ba. Haka shi ma kulob din Isma’il SK Rum tuni ya bayar da sanarwar dage shi daga yin wasanni har sai abin da hali ya yi a kan wannan mugun hali da ya nuna.
Manajan kulob din SK Rum Mista Micheal Massner ya bayyana takaicinsa a kan wannan danyen aiki da Isma’il ya aikata kuma ya ce tilas su dauki mataki a kan dan kwallon don ya zama darasi ga na baya.
Sai dai dan kwallo Isma’il Gunduz ya ce wannan hukunci da aka dauka a kansa ko a jikinsa kuma ya sha alwashin daukaka kara a kotun sauraron kararrakin kwallo don cigaba da yin wasa ba tare da wata matsala ba.
Ya ce ba da gangan ya yi wa alkalin wasan karo ba, santsi ne ya kwashe shi a kokarinsa na kai kuka ga alkalin wasan da hakan ta sa ya yi masa karo a bisa kuskure.
An dage dan kwallo wasanni 70 don kai wa alkalin wasa karo
An dage wani dan kwallo mai suna Isma’il Gunduz da ke buga kwallo a gasar rukunin ’yan dagaji (amateur) da ke kasar Austiriya bayan ya…