✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage dakatarwar da aka yi wa FC Barcelona a kan cinikin ’yan kwallo

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta dage dakatarwar da ta yi wa kulob din FC Barcelona da ke Sifen…

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta dage dakatarwar da ta yi wa kulob din FC Barcelona da ke Sifen a kan saye da kuma sayar da ’yan kwallo har na tsawon shekara biyu.
Hukumar ta ce hakan ya faru ne bayan da kulob din ya daukaka kara a game da hukuncin dakatarwar da aka yi masa.
Hukumar ta ce an dage hukuncin ne har sai bayan an saurari karar da kulob din ya kai a gaban kotun daukaka kara don haka a yanzu kulob din yana da damar yin ciniki saye ko sayar da ’yan kwallonsa ba tare da wata matsala ba.
A watan da ya gabata ne dai Hukumar FIFA ta bayar da sanarwar dage kulob din daga yin cinikin ’yan kwallo har na tsawon shekara biyu.  Hukumar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan da aka samu kulob din da laifin rashin bin ka’idar yin cinikin ’yan kwallo musamman wadanda ’yan kasa kasa da shekara 18.
“Kulob din FC Barcelona ya daukaka kara a kan hukuncin dakatarwar da aka yi masa na saye da kuma sayar da ’yan kwallo wanda Kwamitin ladabtarwa na hukumar ya yi masa don haka yanzu za a zartarwa kulob din hukunci ne bayan an gama sauraron daukaka kararsa”, inji sanarwar da Hukumar ta fitar kuma ta watsa a kafar sadarwata a shekaranjiya Laraba.
Da yawa daga cikin magoya bayan kulob din sun nuna rashin jin dadinsu a lokacin da Hukumar FIFA ta kakaba wa kulob din hukuncin kin saye da sayar da ’yan kwallo na na tsawon shekara biyu  musamman a wannan lokaci da kulob din ya fada mawuyacin hali a harkar wasan kwallo.