✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cimma matsaya kan rikicin Sudan

Majalisar Soji mai mulki a Sudan da shugabannin adawa sun saka hannu a wata yarjejeniyar raba iko bayan kashe dare suna tattaunawa. Kamar yadda BBC…

Majalisar Soji mai mulki a Sudan da shugabannin adawa sun saka hannu a wata yarjejeniyar raba iko bayan kashe dare suna tattaunawa. Kamar yadda BBC ya ruwaito.

An sa hannu a kan yarjejeniyar ce a Khartoum, babban birnin kasar a gaban masu shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Afirka.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito Mohamed Mohamed Hamdan “Hemeti” Dagolo na cewa wannan wani al’amari ne na tarihi a kasar.

Ya ce “Ina farin cikin yi wa mutanen Sudan albishir kan wannan babban al’amari na saka hannu kan yarjejeniyar siyasa.”

Sojoji sun kwace mulki ne bayan hambarar da Omar al-Bashir a watan Afrilu.

Ana sa rai wannan yarjejeniya za ta kawo karshen tashin hankalin da kasar ta fuskanta a baya-bayan nan, kuma za a kafa gwamnati havin gwiwa ta shekara uku; inda daga karshe za a gudanar da zabe.

Sai dai wata mai magana da yawun vaya daga cikin manyan kungiyoyin fararen hula ta nuna halin ko in kula kan yarjejeniyar.

“Ba wani abin a-zo-a-gani ba ne,” inji Dokta Sara Abdelgalil, Kakakin Kungiyar Kwadago ta Sudan Professionals Association.

“Wannan shi ne matakin farko na raba iko, amma babu bayanai sosai a kansa. Mataki na biyu na tattaunawa shi ne ayyanawa a hukumance. Wannan mataki ne na fargaba da fata. Babu wani abin murna a cikinsa.” Kamar yadda BBC ta ruwaito ta.