Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Bauchi ta ci tarar wani direban motar haya saboda saba matakan kariyar COVID-19.
Kwamandan Hukumar a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN, a ranar Laraba.
- An rufe asibiti saboda jinyar masu COVID-19 ‘mai tsanani’ a Kano
- Najeriya za ta sayi rigakafin COVID-19 miliyan 120 —Fayemi
- An rufe babbar kasuwar Abuja saboda karya dokar COVID-19
- ’Yan sanda za su fara dirar mikiya a kan masu karya dokokin kariyar COVID-19
“A wannan karon da COVID-19 ta sake bulla, muna son tabbatar da cewa tashar motoci na bin matakan da NCDC ta kafa.
“Mun kama wata mota da lambar Jihar Legas da ta karya doka wajen diban fasinja fiye da kima.
“An rubuta wa diraben tarar N26,000 saboda rashin ba da tazara da kuma rashin mallakar lasisin tuki.
“Wannan zai zama darasi ga sauran direbobi da ke bijire wa dokokin kariyar COVID-19,” a cewar Abdullahi.
Kwamandan ya jadadda cewa jami’an Hukumar za su ci gaba da kama direbobi masu saba dokokin da aka shimfida na hana yaduwar cutar.