An shiga firgici da safiyar Alhamis ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata.
Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin ruwan. Wutar ta bazu cikin masaukin fasinjoji da sauri ta kama wasu fasinjojin da ke ciki.
- Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato
- INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye
“Akwai wani babban abin fashewa daga ɓangaren injin jirgin wanda hakan ya haifar da gobara wadda ta laƙume jirgin.
Majiyar ta ƙara da cewa, “har yanzu ba a san abin da ya haddasa tashin wutar ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike”.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Jihar Legas (LASWA), ta ce fasinjoji huɗu ne kawai suka samu raunuka daban-daban.
“Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Jihar Legas (LASWA) ta tabbatar da wata gobara da ta tashi da misalin ƙarfe 6:45 na safiyar yau a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, ɗauke da jirgin LAGFERRY mai suna “Igbega Eko” da ke kan hanyarsa ta zuwa tsibirin Ɓictoria Island.
“Bayan samun kira na ɓacin rai, jami’an masu bayar da agajin gaggawa ta LASWA cikin hanzari suka tashi zuwa wurin, suna aiki tare da haɗin gwiwa tare da LAGFERRY, masu gudanar da aikin kwale-kwale da sauran masu ba da agajin farko don gudanar da lamarin yadda ya kamata.
Mun yi farin cikin bayar da rahoton cewa an kwashe dukkan fasinjoji da ma’aikatan da ke cikin jirgin cikin ƙoshin lafiya, kodayake fasinjoji huɗu sun samu raunuka kuma a halin yanzu suna samun kulawar jami’an kiwon lafiya.