Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar.
Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin Ikorodu tana kan hanyar zuwa CMS a lokacin da lamarin ya faru.
- Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang
- An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe
Ya zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton, masu bayar da agajin gaggawa da suka haɗa da jami’an ’yan sandan Nijeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA), da jami’an kashe gobara da jami’an tsaro na yankin, sun isa wurin domin shawo kan gobarar.
Ɗaya daga cikin fasinjojin motar ta shaida wa majiyar cewa gobarar ta tashi ne a matsayin hayaƙi daga ɓangaren direban.
A cewarta, tun farko fasinjojin sun yi tunanin hayaƙin ya fito daga wasu motocin bas ɗin; duk da haka, ba da daɗewa ba hayaƙin ya ƙara tsananta, hakan ya sa su cikin yanayin firgita.
“Da muka ga hayaƙin ya yi yawa, nan take muka fito daga motar bas ɗin kafin wutar ta tashi”, ta ƙara da cewa babu wani daga cikin fasinjojin da ya samu wani rauni.
Ta ƙara da cewa direban motar ya gudu bayan tashin gobarar.
“Direban da kwandastan sun gudu, ba su ma jira su ga abin da zai same mu ba.
“Tabbas, sun san abin da ya faru, sun san motar bas ɗin ba ta da kyau kafin su saka fasinja su bi hanya kuma sun jefa rayuwarmu cikin haɗari,” in ji ta.