Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Najeriya NAPTIP ta ce jami’anta sun ceto wadansu ’yan mata da aka yi safarar su daga Najeriya a kasar Indiya.
NAPTIP ta ce ta samu wannan nasara ce tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Ofishin Jakadancin Najeriya da ke birnin New Delhi a kasar Indiya, da kuma ’yan sandan birnin na New Delhi.
A wata sanarwa da Hukumar ta aika wa Muryar Amurka, ta ce an ceto matan a hannun wata mata mai safarar mutane ta kasa da kasa mai suna Joy Shandy Okah ’yar Najeriya.
Sanarwar ta ce an cafke Joy Shandy a birnin na New Delhi yayin da aka ceto wasu ’yan mata guda uku da ta kai su kasar Indiyan ta kuma tilasta masu yin karuwanci.
Bisa ga bayanin hukumar, kafin dauko su daga Najeriya, sai da matar ta sa ’yan matan suka yi rantsuwa kafin ta kaisu India, sannan bayan sun isa can kuma ta kwace wayoyin salularsu da takardunsu na bulaguro.
Muryar Amurka ta ce matar ta tilastawa ’yan matan wadanda aka tabbabar sahihancin takardun bulaguron nasu ’yan asalin jihohin Kuros Riba da Edo ne a Kudu maso Kudancin Najeriya.
Bayanai sun ce sai da kowacce daga cikin ’yan matan suka yi biyanta Naira miliyan hudu da dubu dari biyar ta hanyar yin karuwanci kafin jami’ai su kubutar da su a watan Fabrairu na wannan shekara.
Tuni kuma ’yan sandan birnin New Delhi suka kammala bincike nan take inda kasa da awa 24 aka gurfanar da ita gaban kotu don fuskantar shari’a.