Wasu rahotanni na cewa an ceto shida daga cikin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Wata majiyar soji ce ta tabbatar da hakan, biyo bayan farmakin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Sabon-Gida da ke Karamar Hukumar Bungudu.
- Sojoji sun gano masana’antar ƙera bindigogi a Kudancin Kaduna
- Jamus ta naɗa Julian Nagelsmann kociyan tawagar ƙasar
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar waɗanda suka isa unguwar Sabon Gida da tsakar dare, sun riƙa harbe-harbe kafin su yi awon-gaba da ɗaliban.
Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Umar Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayyana adadin ɗaliban da aka yi garkuwar da su ba.
Sai dai Gwamnatin Zamfara ta tabbatar cewa dalibai 35 ’yan ta’addan suka yi awon gaba da su a dakunan kwanansu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami’in gwamnatin jihar yana tabbatar da sace daliban a wasu uku daga cikin dakunan kwanan dalibai kafin asubahin ranar Juma’a.
Wannan shi ne adadi mafi yawa na dalibai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokaci guda a bana.
Wata majiya ta ce maharan sun yi musayar wuta da sojoji, amma duk da haka sun tafi da daliban da suka sace.
Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi jigata daga ayyukan ƴan bindiga masu fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Ko a cikin watan Fabarairun 2021, ƴan bindiga sun shiga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a jihar, inda suka sace ɗalibai mata 317.
Haka nan ma a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.