An ceto kimanin mutum 30 da ransu daga cikin fasinjoji kusan 200 da jirgin ruwa ya kife da su a Jihar Kebbi.
Suleman Bobo daga cikin masu aikin ceto ya ce an kuma gano gawarwaki 46 da suka nutse bayan hatsarin jirgin da ke dauke da mutanen da yawancinsu masu sana’ar hannu ne da ’yan kasuwa.
- N-Power: Za mu dauki rukuni na uku —Minista
- Janar Farouk Yahaya ya zama Babban Hafsan Sojin Kasa
- Uba ya yi wa ’ya’yansa uku fyade
“Kawo yanzu an gano gawarwaki 46, an kuma binne su, banda wadanda aka ceto a cikin dare,” inji Suleiman wanda shi ne Shugaban matasa garin Warra.
Suleman ya ce 23 daga cikin gawarwakin an gano su ne a garin, sauran kuma a wasu kauyukan da ke makwabtaka da su.
Ya shaida mana cewa a ranar Laraba, an gano gawarwaki biyar, a ranar Alhamis kuma an gano wasu 41.
Aminiya ta gano cewa masu aikin ceto ne suka gano 45 daga cikin gawarwaki, ta karshe kuma an gano ta ne bayan da ruwa ya dago ta.
Wakilinmu ya ziyarci wurin da ake aikin ceton bayan aukuwar hatsarin, inda ya iske daruwawan matasan garin na Warra suna kai-komo wajen gudanar da aikin ceto.
Jirgin ruwan ya kife da fasinjojin ne a yankin Tsohuwan Lambata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi a hanyarsa ta kai fasinjojin Jihar Neja.