Jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya sun ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja da wasu ’yan bingida suka yi awon gaba da su a ranar Talata.
Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindiga sun kutsa kai rukunin gidajen ma’aikatan jami’ar inda suka yi awon gaba da wani adadi na mutane da bayanai suka ce ba su wuce shida ba ciki har da Farfesoshi biyu.
- Real Madrid ta ci kwallo 1,000 a gasar Zakarun Turai
- Aminiya a kauyen su Shekau: Tun yana yaro fitinanne ne — Dagaci
Rahotanni sun bayyaa cewa, masu garkuwa da ma’aikatan jami’ar sun nemi fansar Naira miliyan 300 daga hannun ’yan uwan wadanda abin ya shafa.
Sai dai cikin wani sako da ya wallafa safiyar Juma’a a shafinsa na Facebook, wani ma’aikacin jami’ar, Dokta Abubakar Kari, ya ce an ceto duk mutanen da aka sace ba tare da biyan ko asi na kudin fansar da ’yan bindigar suka nema ba.
Yana cewa, “Allah Ya karbi addu’o’inmu, ku taya ni yi wa Allah Godiya da bayyana farin ciki domin kuwa wadanda aka yi garkuwa da su sun kubuta.
“A yanzu haka muna kan hanyar zuwa asibiti tare da su domin tabbatar da ingancin lafiyarsu.”
Mai Magana da Yawun ’Yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da ingancin rahoton ba tare da yin wani karin bayani a kai ba.
Sai dai ta tabbatar wa da wakilinmu cewa, sun samu nasarar cafke wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da ma’aikatan jami’ar.