Rundunar hadin guiwar jami’an tsaro ta ceto wani yaro dan shekara biyu da kuma wasu mata ’yan kasuwa 11 da ’yan bindiga suka sace a Jihar Kwara.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Ajase zuwa Ipo bayan an yi musu kwanton bauna da dare a lokacin da suke dawowa daga kasuwar Oke-Ode da ke Ifelodun, inda suka je kasuwanci a Larabar da ta gabata.
An ce ’yan kasuwar sun fito ne daga yankunan Offa, da Yaaru da kuma Ikirun da ke jihohin Kwara da Osun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda a Jihar Kwara, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a daren ranar Talata.
Kodinetan kungiyar tsaro ta hadin gwiwa a yankin Kwara ta Kudu, Olaitan Oyin-Zubair, ya yaba da irin jajircewar da mafarauta da ’yan banga suka yi wurin kubutar da wadanda aka sace.
Ya kara da cewa wadanda aka sace mata ne ’yan kasuwa wasu sun kubuta kwana guda bayan faruwar lamarin yayin da aka ceto sauran ranar Talata.
Ya bayyana cewa ba a bayar da kudin fansa ga kowa ba.
Oyin-Zubair ya bukaci jami’an tsaro da ’yan farauta da ’yan banga su ci gaba da yin aiki tare domin fatattakar ’yan bindiga a yankin Kwara ta Kudu da jihar baki daya.