Saboda fitar da Ghana da aka yi a Gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil ta sa shugaban qasar John Dramani Mahama ya bayar da sanarwar canza wa Ministan harkokin wasanni da matasa da kuma mataimakinsa wajen aiki. Idan za a tuna Ghana dai ta kasa kai bantenta ne a rukunin da ta fafata da qasashen Amurka da na Fotugal da kuma Jamus a gasar cin kofin duniya a Brazil. A rukunin, Ghana ta samu rashin nasara ne a wasansu da Amurka sannan ta yi kunnen doki da ci 2-2 da Jamus yayin da Fotugal ta doke ta da ci 2-1 a da hakan ya sa aka fitar da ita tun a matakin farko. Jim kaxan bayan an fitar da qasar daga gasar ce sai shugaban qasar ya ba da sanarwa a ranar Asabar ta makon jiya cewa an canza wa Ministan kula da harkokin matasa da wasanni Elvis Afriyie-Ankrah wurin aiki daga Minista zuwa qaramin Minista a fadar shugaban qasa. Haka shi ma mataimakinsa Joseph Yamnin an koma da shi qaramin Minista mai kula da yankin Ashanti”. Sanarwar ta ce an yi waxannan canje-canje ne a qoqarin da gwamnatin Mahama take yi don farfaxo da harkokin wasanni musamman vangaren qwallon qafa a qasar. Idan za a tuna Hukumar qwallon qafar Ghana (FA) ta samu matsala da biyu daga cikin ’yan qwallon qasar watau Kevin-Prince Boateng da Sulley Muntari ana gab da yin wasa a tsakanin qasar da Fotugal a gasar cin kofin duniya a makon jiya al’amarin da ya sa aka sallami ’yan qwallon kuma suka kama gabansu tun kafin wasan ya gudana. A wasan Ghana ta samu rashin nasara ne da ci 1-2 da hakan ya sa ta kasa hayewa zagaye na biyu.
An canza wa Ministan wasanni wajen aiki saboda fitar da Ghana
Saboda fitar da Ghana da aka yi a Gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil ta sa shugaban qasar John Dramani Mahama ya…