Wani mutum ya kutsa kai cikin masallaci sannan ya caka wa limamin da ke jagorancin sallar Asuba wuka a birnin New Jersey na Amurka, Imam Sayed Elnakib.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, lokacin da Musulmai ke sallar Asuba a masallacin Omar a watan Ramadan.
- Buhari zai tafi Saudiyya don yin Umararsa ta karshe a matsayin Shugaban Kasa
- Birtaniya ta dakatar da daukar ma’aikatan lafiya daga Najeriya
Hakan dai ya sa limamin mai shekara 65 ya ji mummunan rauni, kodayake rahotanni sun ce yana samun sauki a asibitin da aka kwantar da shi.
Sai dai nan take mutanen da ke sallah a masallacin suka yi ta maza suka cafke mutumin mai suna Serif Zorba, mai kimanin shekara 32.
Kyamarorin tsaro dai sun nuna yadda mutumin ya kutsa masallacin lokacin da masallata suka yi sujjada sannan ya daba wa limamin wuka.
Maharin dai ya fita da gudu bayan harin, amma mutane sun sami nasarar yin ram da shi, har sai da ’yan sanda suka isa wajen sannan suka damka shi gare su.
“Limamin yana cewa wayyo ya kashe ni. Ku yi kokari ku kama shi,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa kafar yada labarai ta CBS da ke Amurkan. “Yana ta zubar jini bayan raunin da aka ji masa a wuya.”
A cewar Abdul Hamdan, Kakakin masallacin, akwai masu ibada kimanin 200, kuma an caka wa limamin wuka akalla sau biyu.
Sai dai Kakakin ya ce wanda ya kai harin wasu daga cikin masallatan sun ce fuskarsa ba bakuwa ba ce a yankin, amma babu wanda ya iya gane shi daga cikin mahukuntan masallacin.