Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani mutum dauke da Katin Zabe 29 a yankin Karamar Hukumar Dawakin Tofa da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa Aminiya da hakan, inda ya ce lamarin ya faru ne a Hayin Hago.
- Alhaji Bako Zuntu ya riga mu gidan gaskiya
- Diphtheria: Abubuwan da ya kamata ku sani game da bakuwar cutar da ta kashe mutum 25 a Kano
Kiyawa ya ce an mika wanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar wanda bayan kammalawa za a gurafanar da shi a kotu.
A hannu daya, Jam’iyyar NNPP ta yi zargin wanda aka cafken dan Jam’iyyar APC ne, kuma wai yana aiki ne bisa umarnin Abba Ganduje.
Abba Ganduje da yake ga Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, wanda kuma yake takarar dan Majalisar Wakilai a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a jihar.
Jigo a yakin neman zaben NNPP a jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi zargin wanda lamarin ya shafa ya tabbatar musu Abba ne ya ba shi aikin tattaro Katin Zabe inda za a raba wa masu katin N10,000 kowannensu.
Sai dai Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Shehu Maigari, ya ce zargin da NNPP ta yi abu ne mara tushe, musamman ma idan aka yi la’akari da dokar nan ta zabe da ta ce babu wanda zai iya kada kuri’a da Katin Zabe fiye da sau daya.