Rundunar ’Yan sanda a jihar Katsina ta cafke wata uwa mai sana’ar karuwanci da ake zargi da sayar da jaririyarta ’yar wata hudu da haihuwa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Isah Gambo ne ya tabbatar da faruwan hakan yayin zantawa da Aminiya a ranar Litinin.
- Dalilin da ya sa Kotu ta kawo karshen shari’ar Naziru Sarkin Waka
- Yadda aka ceto mata 4 masu ciki a gidan sayar da jarirai
SP Gambo ya ce an kama wadda ake zargi mai shekara 25, wadda ake wa inkiya da Justina, inda ta hada baki da wata kawarta, wajen sayar da jaririyarta a kan Naira dubu 300.
Ya ce: “A ranar 26/11/2020 da misalin karfe 4:30, rundunar ta samu nasarar cafke wata mata ’yar shekara 25 ’yar asalin Jihar Adamawa amma tana zaune a Kofar Kaura Layout a Jihar Katsina.
“Ta hada baki da wata kawarta, ’yar shekaru 32 mazauniyar Kofar Kaura ’yar asalin Jihar Delta.
“Sun siyar da jaririyarta ’yar wata hudu a kan Naira dubu 300 ga wata mata mai shekar 43 ’yar asalin Karamar Hukumar Ekuisigo ta Jihar Anambra,” inji Gambo.
Ya kara da cewa, ana tsaka da bincike ne aka gano wani dan uwan wadda ta sayi jaririyar, wanda aka hada baki wajen shuka wannan tsiya.
SP Gambo ya ce an samu N165,000 a hannun Justina yayin da kuma N85,000 a hannun Ruth a matsayin wani kason kudin da suka samu wajen sayar da jaririyar yayin da ake ci gaba da bincike.