✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke mutum biyu da jabun kudi a Kwara

Dubun masu amfani da jabun kudin ta cika yayin da jami'an tsaro suka cafke su.

Jami’an Hukumar Farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC) sun cafke wasu mutum biyu da aka samu da jabun kudi a Kasuwar Yagba ta Jihar Kwara.

Wannan na dauke ne cikin jawabin da Kakakin Hukumar na Jihar, Babawale Zaidu, ya fitar ranar Asabar a Ilorin, babbab birnin Jihar.

“Wanda ake zargin sun bayyana cewar za su shiga kasuwar Yagba ta yadda ba kowa zai gane su ba.

“Mutum biyun yanzu haka suna hannun jami’anmu inda ake gudanar da bincike a kansu,” a cewar Zaidu.

Zaidu ya ce jagoran masu jabun kudin wanda ya tashi a jihar Ebonyi, mazaunin Kwara ne wanda wani mutum ya dora sa a kan harkar jabun kudi a birnin Lokoja.

Ya ce ababen zargin sukan zaga kasuwanni daban-daban inda suke shigar da jabun kudaden nasu ta yadda ba za a gane ba.