✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke Matashin da ya yanke wa ’yar shekara 6 mafitsara a Bauchi

Ba ni kadai na aikata laifin ba.

Wani matashi da ake zargi da yankewa ’yar shekara 6 mafitsara a Karamar Hukumar Jama’are ta Jihar Bauchi  mai suna Abdulkadir Wada Haladu,  ya fada komar jami’an ’yan sanda a Jihar Nasarawa.

Mai magana da yawun rundunar ’yan jihar, AM Wakili ne ya gabatar wa da manema labarai wanda ake zargi.

AM Wakili ya ce “bayan mun fadada bincike, jami’anmu sun samu nasarar cafke matashin a yankin Mararraba na Jihar Nasarawa.”

“Sai dai an samu sabanin bayani a tsakaninsa da wani matashi da ake zargi dan shekara 19 wanda ya fara shiga hannunmu.”

Aminiya ta samu cewa wani matashi dan shekara 19 mai suna Abdurra’uf wanda shi ma ake zarginsa kuma ya shiga hannu tun da farko, ya ce Abdulkadir ne ya yi amfani da wuka wajen yanke gaban yarinyar mai shekaru shida kacal a duniya.

Daga bisani bayan da Abdulkadir ya shiga hannu, ya ce sun yi tarayya ne da Abdurra’uf wajen aikata wannan mummunar ta’ada.

A jawabin da matashin ya bai wa jami’an ’yan sanda yayin da ya ke amsa tambayoyi, ya ce sun yi amfani da karfin tsiya wajen makure yarinyar har ta suma sannan suka kai ta wani kango inda a nan suka yanke mata gaba.

%d bloggers like this: