Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta cafke wata mata mai shekara 30 da ake zargi da kashe jabun kudi na Naira dubu daya a kasuwar Kila da ke Karamar Hukumar Odeda a Jihar.
Kakakin rundunar a Jihar, Abimbola Oyeyemi ne, ya tabbatar wa maneman labarai hakan a Abeokuta ranar Juma’a.
- Shugabannin Hausawa sun fara gyara wa fitsararru zama
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Daba Ke Juya Akalar Siyasar Najeriya
Ya ce, “Bayan gudanar da bincike, mun gano jabun kudi har N24,000 a cikin jakarta.
“Bayan tuhumarta, ta bayyana cewar ta na hada jabun kudi da masu kyau sai ta shiga kasuwa ta yi sayayya,” a cewar Oyeyemi.
Kakakin ya kuma ce bayan samun rahoton da jami’an ’yan sandan Jihar suka yi, sun shiga bincike yayin da daga karshe suka yi nasarar cafke ta.
Kazalika, kakakin ya ce bincikensu ya gano jami’an tsaro sun kama matar a lokuta daban-daban kan laifin amfani da jabun kudi a kasuwannin Abeokuta.
Abimbola ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin mayar da ita Sashen Binciken Manyan Laifuffuka, don fadada bincike.