✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke matar da ake zargi da safarar ’yar shekara 15 zuwa ketare

Rundunnar ’Yan Sandan Jihar Delta ta cafke wata mata wacce ake zarginta da hannu a safarar wata budurwa daga jihar zuwa kasar Ivory Coast.

Rundunnar ’Yan Sandan Jihar Delta ta cafke wata mata wacce ake zarginta da hannu a safarar wata budurwa mai shekaru 15 daga jihar zuwa kasar Ivory Coast.

Matar dai wacce daliba ce a Makarantar Sakandaren Ugnomro dake Karamar Hukumar Uvwie da ke jihar, an ce ta cika wandonta da iska ne bayan an zarge ta da aikata laifin.

Wata majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa matar ta fara nuna bakin alamu ne a watan Satumbar 2020 kafin daga bisani ta gudu daga zuwa yankin Alaka.

Majiyar ta ce, “Mun dauke ta zuwa Babban Asibitin da ke Ekpan bayan ta fara nuna bakin alamun, amma likitan da ya duba ta ya ce lafiyarta kalau. A wancan lokacin, mun dauke ta zuwa coci don kubutar da ita, kwana biyu kuma ta sake dawowa hayyacinta.

“Kwatsam sai ta sake fita daga gidan zuwa Alaka kuma wannan shine karo na karshe da muka ganta. Kawai sai ji muka yi ta kira mu daga Legas, daga nan kuma sai Ivory Coast.

“Lokacin da aka sake bude iyakokin kasa a cikin watan Disamba, sai wadanda suka dauketa zuwa can suka fara kiran wayar mahifiyarta suna neman kudi kafin su yarda su dawo da ita Najeriya.

“An yi iya kokarin ganin an dawo da ita hannun Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP), sannan kuma mun kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an cafke ta bisa zargin da safarar wasu‘ yan mata a yankunan Uvwie da Orerokpe na jihar.

Ta ce tuni aka tura lamarin daga ofishin ’yan sanda na Orerokpe zuwa ga shalkwatar rundunar don ci gaba da bincike.