Hukumar Shige da Fice ta Kasa (Immigiration), reshen Jihar Katsina, ta cafke wasu masu safarar mutane biyu tare da tseratar da mutum 18.
Kwanturolan Hukumar na Jihar, Abdulrazak Muazu ne ya sanar da hakan yayin gabatar da wadanda ake zargin a shalkwatar Hukumar da ke Katsina.
- An shiga rudani a Kaduna kan umarnin bude makarantu
- Zazzafar muhawara ta barke a Majalisa kan wani sabon kudiri
- Saudiyya ta wajabta wa alhazai karbar rigakafin COVID-19
- An dage auren amaryar da ta bata gab da bikinta
“Masu safarar mutanen da wadanda aka ceton, dukkaninsu sun fito daga jihohin Edo, Osun, Ogun, Legas da Delta.
“Wanda aka tseratar da suka hada da mata 12 da maza takwas, shekarunsu 3 zuwa 45.
“An yi kokarin ketare iyakar Najeriya daga Jibiya zuwa Agadez da ke Jamhuriyar Nija, inda daga nan za su tsallaka zuwa kasar Libiya,” inji Muazu.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a yayin wani sintiri a garin Charanchi, bayan bayanan sirri.
Ya kara da cewa wanda ake zargin namiji mai shekara 32 da mace mai shekara 35, sun kulla auren bogi a tsakaninsu don safarar mutanen zuwa kasashen ketare.
Sai dai a yayin samamen da suka kai daya daga cikinsu ya tsere tare da barin motarsa kirar Citron 806.
Kwanturolan ya ce za a mika wadanda ake zargin da wadanda abin ya ritsa da su zuwa ofishin shiyya na Hukumar Hana Fataucin Mutane (NAPTIP), don ci gaba da bincike.