✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke masu garkuwa da ’yan fashi 23 a Filato

Ana zargin mutane 23 da aikata fashi da makami garkuwa da mutane.

Hadin gwiwar jami’an tsaron Operation Safe Haven sun  kame mutum 23 da ake zargi da aikata fashi da garkuwa da mutane.

Kwamandan Rundunar, Manjo-Janar Dominic Onyemelu, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da wandada ake zargin ga manema labarai a Jos.

“Wadanda aka cafke din an same su dauke da muggan makamai da suek amfani da su wajen aikata laifuka daban-daban,” a cewar Onyemelu.

Ya ce 17 daga cikin wadanda aka cafke din, ana zargin su da laifin yin garkuwa da mutane, hudu kuma laifin fashi da makami, sai ragowar biyun da ake zargi da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Onyemelu, ya ce dole ne sai mutane sun taimaki jami’an tsaro, sannan za rika samun nasarar dakile miyagun ayyukan bata-gari.