’Yan sanda sun cafke wata mata da ake zargi ta yi wa jaririnta dan wata 11 yankan rago a kauyen Yonen da ke Karamar Hukumar Yakurr ta Jihar Kuros Riba.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Irene Ugbo ce ta tabbatar da faruwar hakan ranar Laraba a Kalaba, babban birnin jihar.
- An yi zanga-zanga kan hana Adaidaita Sahu bin wasu titunan Kano
- Najeriya ba ta yin abin da ya dace wajen rage yawan haihuwa – Hukumar Kidaya
Ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Talata kuma ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka dauki haramar sauke nauyin da rataya a wuyansu.
A cewarta, shigar ‘yan sanda batun a kan kari ya sa matar ta kubuta daga fushin mutanen gari.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, matar ta yi amfani da adda ce wajen yanke kan jaririn.
Bayanai sun ce wani yaron matar ne ya kwarmata wa jama’a abin da ya faru bayan da ya gane wa idanunsa danyen aikin da mahaifiyarsa ta aikata.
Sai dai babu wani cikakken dalili a kan abin da ya sa matar ta dauki wannan mummunan mataki a kan jaririn.
Sarakunan yankin sun ce duk da dai al’amarin ya kada su, amma sun yi kira ga al’ummar da a zauna da juna lafiya ba tare da wani tunanin daukar matakin fansa ba, yayin da ‘yan sandan suka ba da tabbacin za su zurfafa bincike kan lamarin.
(NAN)