✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke lauya kan lakada wa matarsa duka

Wani lauya ya shiga hannun hukuma kan zargin lakada wa matarsa dukan kawo wuka a Jihar Akwa Ibom.

Wani lauya mai ya shiga hannun ’yan sanda kan zargin lakada wa matarsa dukan kawo wuka a Jihar Akwa Ibom.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga Barista Sunday Ebong yana dukan matarsa, daga ita sai ’yar riga da dan kamfai a jikinta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, SP Odiko MacDon, ya ce “an kama Barista Ekeere Sunday Ebong ne bisa zargin lakada wa matarsa duka aka baza a kofofin sada zumunta, inda aka ga ya ji mata rauni lokacin da yake dukan ta, ya farfasa mata jiki.”

Kazalika ana zargin Barista Sunday da kasancewa mutum mai yawan cin zarafin matarsa.

Wata kungiya Mai fafutukar kwato ’yancin mata ta sha alwashin bin shari’ar domin ganin an yi  wa lauyan hukunci dai dai da abin da ya aikata.

SP MacDon ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya sha alwashin ganin an hukunta duk wanda ake zargi da cin zarafin iyalinsa ko na wani a jihar.

Rundunar ta ce ana ci gaba da binciken wanda ake zargi da yi wa matarsa dukan kawo wuka kuma da zarar an gama bincike ko tu za a mika shi.