Wani magidanci da ake zargin ya yi tafiyayya zuwa wurin karuwarsa a Jihar Bayelsa daga Jihar Delta ya gamu da ajalinsa a ɗakinta.
Bayanai sun ce, wannan mamaci, yana fama da larurar shanyewar ɓarin jiki.
- Harajin tsaron Intanet: ‘Gwamnatin Tinubu ba ta da tausayi’
- Ya yi mutuwar ƙarya don ƙin biyan kuɗin makarantar ɗansa
Haka kuma majiyar labarinmu ta tabbatar cewa magidancin, mai kimanin shekara 40 a duniya yana da ’ya’ya 12 da ya baro ya je Bayelsa wurin farkar tasa.
Duk ƙoƙarin da jama’a suka yi na gano dangi ko ’yan uwansa ya ci tura, ƙarshe dai sai hukumar tsaro aka sanarmawa.
Ya zuwa rubuta wannan labari babu ɗan uwa ko dangin mamacin da ya rasu a ranar Talatar da ta gabata da ya bayyana kansa.
Lamarin dai ya jefa karuwai da ke unguwar cikin zullumi da firgici har ta kai su ga kwashen komatsensu suna ɓoyewa saboda ba su da tabbas a kan abin da hukuma za ta yi idan har aka zo binciken.
Kwamandan ’Yan Sintiri (VGN) na Jihar Bayelsa, Tolumobofa Akpoebibo Jonathan, ya shaida wa manema labarai cewa mamacin mai kimamin shekara 40 na da ’ya’ya 12, kuma ya je Yenagoa ne takanas daga Jihar Delta wajen farkar tasa.
Majiyar ’yan sanda ta tabbatar wa wakilinmu mutuwar mutumin, wanda aka sakaya sunansa.
ASP Musa Mohammed, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa, ya shaida wa Aminiya cewa suna bincike don gano ainihin sanadiyar mutuwar mutumin, wanda ake zato cutar shanyewar ɓarin jiki ce ta yi sanadin mutuwarsa a ɗakin farkarsa.