Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun sace wata mota ɗauke da wani yaro ɗan shekara uku a yankin Ikenne da ke Jihar Ogun.
An samu rahoton cewa mahaifin yaron, Taiwo Fayobi, ya sauko daga motar ne domin buɗe ƙofar gidansa sai wasu suka yi awon gaba da motar.
- ‘Yaron da ya sayar da ƙodarsa ya sayi wayar hannu ta N290,000’
- Hatsarin Jirgi: Dana Air ya sallami ma’aikata
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wani sako da ta wallafa a shafin sada zumunta na X (twitter) a ranar Asabar.
Omolola Odutola ta ce, “Wani mazaunin Ikenne a Jihar Ogun mai suna Taiwo Fayobi ya ruwaito cewa ya sauko daga motarsa ƙirar Toyota Camry mai PKA 446 GƁ domin buɗe ƙofar gidansa, sai wasu da ake zargin ɓarayi ne su biyu suka tsere da motarsa, tare da yaro ɗan shekara 3 da ke ciki,” in ji ta.
Odutola ta buƙaci masu faɗa a ji a shafukan sada zumunta da su yaɗa wannan batu sosai domin a ceto yaron.
Da take amsa tambayoyi ta ce, “Eh, mai ƙarar ya sauko daga mota ya buɗe kofar shiga gida yayin da motar ke kunne.
“Sai wasu ɓata gari biyu da ba a san ko daga ina suke ba suka shiga motar ƙirar Toyota Camry suka tsere tare da wani yaron ɗan shekara uku yana barci a kujerar baya.”