Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya ta ce ta cafke 114 daga cikin fursunoni 240 da suka tsere daga gidan yari na Kabba a lokacin harin ranar 12 ga watan Satumba, 2021 a Jihar Kogi.
Kakakin hukumar, Francis Enobore, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.
- Masu garkuwa da mutum 5 ’yan gida daya na neman N20m
- Mutum miliyan 1.6 aka yi wa rigakafin COVID-19 a Najeriya
Aminiya ta ba da rahoton yadda wasu ’yan bindiga suka kai hari gidan harin da ke Kabba, a Jihar Kogi, suka saki daruruwan fursunoni.
Tun daga wannan lokaci Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Gidajen Yari, Haliru Nababa, ya ba da umarnin a cafko fursunonin da suka tsere.
“Bayan umarnin Kwanturola-Janar, an yi nasarar sake cafke mutu 114 da suka tsere.
“Babban kwamandan, wanda da kansa ya jagoranci wata tawaga zuwa gidan yarin don gane wa idonsa yadda aka saki fursunonin, ya sa a baza koma don cafke wadanda suka tsere.
“Wannan ya faru ne bayan tsaurara matakan tsaro ta hanyar tura karin jami’an hadin gwiwa da suka yi aiki tukuru” inji sanarwar.
Kazalika, ya bayyana yadda Kwanturola-Janar din ya yaba wa jami’an tsaro kan namijin kokari da suka yi wajen sake kamo fursunoni 114 daga cikin wanda suka tsere.
Ya shawarci wadanda suka tsere din da su mika kansu cikin sa’a 24 masu zuwa ko kuma su fuskanci fushin hukumar.
Ya ce buya da gudu ba zai amfane su ba tunda hukumar na da bayanansu, wadanda tuni aka mika wa jami’an tsaro don tsaurara bincike a kansu.
Ya tabbatar wa jama’ar jihar cewa hukumar za ta ci gaba da kare lafiyarsu, ta hanyar cafke wadanda suka tsere.