✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke daya daga cikin maharan tashar jirgin kasan Edo

Maharan sun kai harin tare da sace fasinjoji akalla 32 a cikin jirgin kasan.

Jami’an tsaro sun cafke wani mutum daya da ake zargi da hannu a harin da aka kai tashar jirgin kasa da ke Karamar Hukumar Igueben a Jihar Edo.

Kwamishinan Yada Labaran jihar, Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan da cewa tun bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro suka bazama cikin dajin da ke daura da tashar jirgin kasan don ceto fasinjojin.

“Mataimakin Gwamnan Edo, Philip Shaibu, ya ziyarci wurin da harin ya faru kuma jami’an tsaro sun shaida masa mutum daya ya shiga hannu daga cikin wadanda suka kai harin, kuma yana taimakon jami’an tsaro da bayanan yadda za a kama sauran da suka kai harin.

“Muna yaba wa ‘yan sanda da sauran jami’an kan yadda suka nuna bajintar aikinsu.

“Muna kumayaba wa mafarauta da sauran jami’an tsaron Edo kan yadda suka taimaka. Wannan kokari nasu ya haifar da kyakkyawan sakamako.

“Muna fatan wannan shi ne karo na karshe da irin wannan harin zai faru a kan dukiyar gwamnati musamman a tashar jirgin kasa a Jihar Edo. Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aikinsu. Muna jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

“Za mu bai wa ‘yan banga da mafarauta cikakken goyon baya don su taimaka wajen gano inda maharan suka buya,” in ji shi.

Kwamishinan ya kara da cewar daya daga cikin fasinjojin da maharan suka yi awon gaba da shi ya kubuta.

Aminiya ta ruwaito yadda maharan suka kai hari tashar jirgin kasan na Edo, inda suka sace akalla fasinjoji 32.