Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga Musulmi masu hannu da shuni su rika taimakon ’ya’yan marasa galihu ta fannin daukar nauyin koyar da su karatun Alkur’ani da ilmin addin tare da ilmin zamani. Ya ce, Allah na kare dukiyar masu bayar da irin wannan taimako daga masifu da sanya wa dukiyar albarka.
Tsohon Shugaban karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, Alhaji Mukhtar Umar Yarima ne ya karanta sakon na Kwankwaso a wajen bikin saukar karatun Alkur’ani na dalibai 27 na makarantar Nurul Islam Kwankwasiya da ke Unguwar Sabo Ibadan. Sanatan ya yi alkawarin bayar da gudunmowar da za ta daukaka darajar makarantar zuwa babbar makarantar koyar da yara ilmin addini da na zamani wanda zai zame masu makamin dogaro da kai a rayuwarsu. Ya ce yana sane da irin sadaukar da kai da malaman makarantar suke yi wajen koyar da dalibai fiye da 500 na makarantar ba tare da biyan su albashi ba. Saboda haka sai ya yi kira ga iyayen yara da attajirai masu hannu da shuni su tashi tsaye wajen bayar da gudunmawa ga gidauniyar makarantar domin ta kai ga cin ma burinta.
Cikin jawabinsa, shugaban makarantar, Khalifa Ibrahim Nahantsi ya jinjina wa Sanata Kwankwaso ne a kan irin taimakon da yake wa makarantar, wanda ya kai ta ga matsayin da take ciki a yanzu. Ya ce hukumar tafiyar da harkokin makarantar ta yanke shawarar sanya sunan Kwankwasiya a cikin sunan makarantar ne saboda irin gudunmowar da yake bayarwa wajen daukaka matsayin makarantar.
daya daga cikin daliban makarantar, dan shekara 16 mai suna Mursadu Ganawi ya haddace Izifi 60 na Alkur’ani a yayin da Mubaishatul Huzali dan shekara 13 ya haddace izifi 30. Sauran dalibai 25 maza da mata sun haddace Izifi daga 10 zuwa 30 ne. Alhaji Mukhtar Umar Yarima shi ne ya mika wa daliban takardun shaida da Allo mai dauke da wasu ayoyin Alkur’ani domin tabbatar da saukar karatun nasu.
Sarakuna da manyan mutane da iyayen daliban da ’yan uwa da abokan arziki daga sassa daban-daban na kasa ne suka halarci wajen bikin da aka gudanar a harabar filin wasa na Lekan Salami da ke Ibadan.