Shugabannin Jam’iyyar APC da ke mazabar Aboro a karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna sun bukaci a soke zaben fidda gwani na kansila da aka yi a mazabarsu, sakamakon rikicin da ya barke a yayin da ake gudanar da zaben a makon jiya.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban mazabar, Zakariya Yahaya da Sakatare, Yahaya Adamu da kuma Shugabar Mata, Rahab danjuma, shugabanniun sun bukaci a kuma hukunta wadanda ake zargi da tayar da rikici lokacin zaben.
Shugabannin sun bayar da shaidar cewa ana cikin zabe ne wadansu matasa suka wargaza zaben, sannan suka gudu da akwatin zabe, inda hakan ya sanya zaben bai kammala ba.
“Amma ga mamakinmu sai aka sanar da cewa dahiru Yunusa ne ya lashe zabe, don haka muna bukatar kwamitin zaben ya gaggauta soke zaben. Domin Gwamnan Jihar Kaduna Nasi.