Gwamnatin Zamfara ta sake bude makarantu bayan wata hudu da rufe su saboda matsalar tsaro da masu garkuwa da dalibai da suka addabi jihar.
A ranar Litinin ne aka koma aji a makarantun da aka rufe tun a watan Satumban 2021 sakamakon garkuwa da dalibai 80 da ’yan bindiga suka yi a wata makarantar sakandare da ke kauyen Kaya a jihar.
“Ana sanar da daukacin shugabannin makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu da ke rukunin launin kore da launin rawaya su koma makarantu daga ranar Litinin (17/01/2022) domin ci gaba da gudanar da harkokin karatau,” injin sanarwar da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar a ranar Lahadi.
Makarantu 115 ne dai gwamnatin jihar ta bayar da umarnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na karatu, sai wasu makarantu 85 da ke rukunin launin ja, da za su ci gaba da kasancewa a rufe, “Har sai yanayin tsaronsu ya inganta,” inji sanarwar.
’Yan bindiga sun daidaita ilimin yara —UNICEF
Yankin Arewacin Najeriya dai na fama da matsalar ’yan bindiga da ke kai hare-hare a kauyuka suna garkuwa da mazauna domin karbar kudin fansa tare da kone gidaje da yin fashi gami da yi wa mata fyade.
Maharan sun sha kai farmaki a kan makarantu suna sace dalibai masu yawa a lokaci guda domin matsa wa gwamnati ko iyayen yaran biyan kudaden fansa.
Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce kananan yara ’yan makaranta akalla 1,500 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantu a Najeriya, kuma 16 daga cikin yaran sun mutu a sakamakon hakan.
An sako yawancin daliban da aka yi garkuwa da su bayan tattaunawa da biyan kudin fansa ga ’yan bindigar, amma har yanzu akwai wadansunsu a hannun masu garkuwa da su.
Yawan garkuwa da mutane ya sa aka rufe daururwan makarantu a jihohi biyar da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da ya hada da jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara, Sakkwato da Jigawa da kuma Jihar Neja a Arewa ta Tsakiya, da nufi kare dalibai daga mahara.
Ayyukan masu garkuwa da mutanen dai na ci gaba da jefa al’ummomin Arewacin Najeriya cikin tashin hankali.
Tun kafin wannan matsala, UNICEF ta ce, yankin shi ne agogon baya wajen yawan kananan yara masu zuwa makarantu.
A halin yanzu, UNICEF na ganin matsalar ’yan bindiga ta hana kananan yara miliyan daya komawa makarantu a kasar da sama da yara miliyan 10 ne ba sa zuwa makaranta, yawancinsu kuma a Arewa.