✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An binne gawarwaki 130 da aka kasa gano ’yan uwansu a Kogi

Yawancin gawarwakin sun shafe wata 7 ba a gano danginsu ba

Gwamnatin jihar Kogi ta binne gawarwaki 130 da aka kasa gano ’yan uwansu bayan sun shafe wata bakwai a Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Lokoja, babban birnin jihar.

Galibin mutanen dai wadanda haduran mota suka ritsa da su ne da wadanda aka kashe a wajen fashi da makami ko garkuwa da mutane.

An binne su ne a wata makabarta da ke Felele a garin na Lokoja.

Shugabar Hukumar Kwashe Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar, Elizabeth Arokoyo, ta ce doka ta dora wa hukumarta hakkin tabbatar tsaftataccen muhalli a jihar ga kowa.

Ta ce sun yanke shawarar daukar matakin ne saboda gawarwakin sun dade a asibitin ba tare da ’yan uwansu sun je nemansu ba.

Wacce ta sami wakilicin mai rikon mukamin hukumar, Ajayi Olufemi, Shugabar ta ce ’yan sanda da jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ne suka kawo gawarwakin.

Elizabeth ta ce sun yi ta shela da sanarwar a kafafen yada labarai don neman ’yan uwan mamatan, amma lamarin ya ci tura.

“Maganar da nake da ku yanzu haka, babu wani daga dangi ko abokan mamatan da suka zo nemansu. Yawancinsu wadanda suka mutu ne ko dai ta sanadin hatsarin mota ko garkuwa da mutane ko kuma fashi da makami.

“Saboda haka ne muka binne su, tun da mun kasa gano danginsu, kuma sun dade a dakin adana gawarwaki ba tare da an gano ’yan uwan nasu ba,” inji ta.