✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bayyana sojojin rundunar tsaron shugaban kasa da aka kashe a Abuja

An bayyana sunayen hafsoshin sojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa da ’yan bindiga suka kashe a Abuja.

An bayyana sunayen hafsoshin sojin Rundunar Tsaron Shugaban Kasa da ’yan bindiga suka kashe a Abuja.

A ranar Lahadi da dare ne ’yan bindiga suka kai wa ayarin sojojin da ke bakin aikinsu harin kwanton bauna suka hallaka uku daga cikinsu, sauran kuma suka sha da kayar.

Kakain Rundunar Soji Mai Tsaron Shguaban Kasar, Kyaftin Captain Godfrey Anebi Abakpa, ya ce sojoji uku ne suka rasu a harin, suna dawowa daga Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke Bwari; ya ce sojoji na shara domin gudanar kakabba bata-gari.

Aminiya ta gano cewa sojojin da aka kashe sun hada da Kyaftin Samuel Attah da kuma Laftanar Ibrahim Suleiman a harin.

Su biyun ’yan asalin Jihar Kogi ne, inda Laftanar Attah ya fito daga Karamar Hukumar Ibaji.

Shi kuma Kyaftin Suleiman ya fito ne daga Karamar Hukumar Olamaboro, kuma mahaifinsa shi ne Kanar Suleiman Ahmodu Babanawa (mai ritaya).

Rahotanni sun ce mahaifinsa ya taka rawar gani kafin ya yi ritaya a ikin soji.