Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira Biliyan 2, 365, 469, 525 domin siyan kayan da za a bukata don gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Janairun badi.
Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar ya ce, “a bisa nauyin da rataya a wuyan gwamnatin jihar na gudanar da mulki, za a raba kudaden tsakanin jihar kuma kananan hukumominta 44.”
Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC), ta ce za ta fara sayar da takardar neman izinin takarar shugabancin Kananan Hukumomi daga ranar 19 ga watan Oktoba 2020.
Shugaban Hukumar KANSIEC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya sanar da hakan yayin bayyana ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomin.
Ya ce, za a gudanar da zaben ne gabanin masu rike da kujerun na yanzu su kammala wa’adinsu.
Kazalika ya ce dokar Hukumar ta 2002 ta yi tanadin cewa a sanar da ranar zabe kwanaki 21 kafin gudanarsa.
Sai dai ya ce a yanzu an sanar kwanaki 90 kafin gudanarsa ne saboda yawan jam’iyyun siyasa da ake da su a jihar Kano domin samun damar aiwatar da duk wani shiri.