dan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu da ake zargi da laifin kashe buduwarsa a shekarar 2013, Oscar Pistoruous ya samu beli har zuwa ranar 18 ga Afrilun badi a lokacin da za a ci gaba da sauraron karar da ya daukaka. Yanzu dai zai koma gidan dan uwansa ne ya ci gaba da zaman daurin talala a can maimakon zaman da yake yi a a gidan yari.
Alkali Aubrey Ledwaba ne ya amince da bayar da belin dan tseren duk da sabuwar tuhumar da ake masa na zargin kashe budurwarsa mai suna Reeba Steenkamp kimanin shekara biyu da suka wuce.
Tunda farko Lauyan Oscar ya bayyana cewa ya kamata kotu ta tausaya masa ganin cewa ya talauce a halin yanzu kuma yana cikin halin ni-’yasu don haka akwai bukatar alkalin ya bayar da belinsa a kudin da ba su taka kara sun karya ba. A nan ne alkalin ya amince da bukatar lauyan inda ya umarci Oscar ya biya Fam 500 kacal a matsayin kudin beli wanda ya yi daidai da Naira dubu 172 da 500, kuma ya biya a ranar Juma’ar da ta wuce kuma aka amince da bayar da belinsa.
Sannan lauyan ya bukaci kotu ta amince wa Oscar ya rika fita shan iska a kowace rana maimakon a yi masa daurin talala a cikin gida na tsawon watanni ba tare da ya leka waje ba. Nan ma kotu ta amince ya rika fita yana zagayawa a kowace rana daga karfe 7:00 na safe zuwa 12:00 na rana.
Sai dai kotun ta haramta masa barin unguwar da yake zaune mai suna Tshwane ba tare da izini ko amincewar kotu ba. Kuma an umarce shi da ya mika fasfonsa sannan kada ya kuskura ya nemi a sabunta masa wani a tsawon lokacin da zai kwashe yana zaman beli. Amma akwai yiwuwar dan tseren nakasassun ya sake komawa gidan yari inda zai shafe akalla shekara 15 idan aka tabbatar da zargin da ake yi masa na kashe budurwarsa a zaman kotun da za a yi a ranar 18 ga watan Afrilun badi.
An bayar da belin Oscar Pistorious
dan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu da ake zargi da laifin kashe buduwarsa a shekarar 2013, Oscar Pistoruous ya samu beli har zuwa ranar…