Jami’an ’yan sanda sun bankado wata haramtacciyar masana’antar kera bindigogin AK-47 na gida a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato.
Kakakin ’yan sanda na kasa, Frank Mba, ya ce jami’an Rundunar da suka kaddamar da samame a haramtacciyar masana’antar sun gano bindigogi kirar AK-47 guda 20.
- Najeriya na zargin Twitter da hannu a fafutikar kafa kasar Biyafara
- Sojoji na fafatawa da mayakan ISWAP a Borno
“Idan ka duba wadannan makaman da miyagun nan suka kera a nan gida, ba su da bambanci da wadanda ake kerawa a kasashen waje.
“Lallai sai ka kai kwararre ne sannan za ka gane bambanci tsakaninsu. Suna aiki da albarusai iri daya,” inji Frank Mba, wanda ya ce, ya ce da ma jami’ansu sun dade suna hakon bata-garin.
Kakakin na Rununar ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba yayin da yake gabatar da wadansu matasa biyu tare da wadansu mutum 79 da ake zargi da aikata muggan laifuka.
Daya daga cikin wadanda ake zargin wanda ya ce ya halarci Kwalejin Fasaha ta Jos, ya shaida wa ’yan jarida cewa a shekara uku, ya kera irin wadannan bindigogi guda 180, ya kuma sayar da kowacce a kan N80,000.
Wanda ake zargin ya ce ya samu horo ne daga tsohon ubangidansa da ya mutu.