Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi barazanar rushe gidajen mutanen da suka kwashe kayan tallafi a jihar matukar ba su dawo da abubuwan da suka diba ba.
Ya bayyana haka ne yayin wani jawabi na musamman da ya yi wa al’ummar jihar ta kafafen watsa labaran jihar ranar Talata.
- Abinda ya sa muka boye kayan tallafi – Gwamnoni
- ‘A kamo barayin kayan tallafin COVID-19 na Kaduna’
- Na yafe wa masu zagi na kan tallafin COVID-19 – Sadiya Farouq
Ya shawarci mutanen da su gaggauta dawo da kayan da suka sata, ko dai daga gwamnati ko daga daidaikun jama’a ga ofisoshin ‘yan sanda mafi kusa da su nan da sa’o’i 12.
Ya ce kin bin umarnin zuwa lokacin da wa’adin zai cika da misalin karfe shida na safiyar Laraba zai tilasta yin bincike gida-gida da zai ba gwamnatin damar rushe duk gidan da aka sami kayan a ciki ko kuma a janye takardar shaidar mallakarsa.
Ya ce, “Wannan wa’adin zai cika ne da misalin karfe shida na safiyar ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba, 2020, bayansa kuma zan sa hannu a kan dokar da za ta ba da damar shiga gida-gida domin fara bincike da karfe bakwai na safe.
“Ya kamata ‘yan kasa nagari su ba jami’an tsaro hadin kai wajen ganin matakin ya sami nasara,” inji gwamna Fintiri.
Gwamnan ya kuma bayyana masu kwasar kayan a matsayin masu laifi, yana mai cewa tuni 155 daga cikinsu suka fada komar jami’an ‘yan sanda.
Fintiri ya kuma ce an cafke wasu motoci guda 9 da babura masu kafa uku makare da irin wadannan kayan tallafin.