Wata kotun majisare mai zamanta a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, ta tasa keyar wasu mutum biyu saboda zarginsu da hannu a kone wani barawo kurmus.
Ana dai zargin Michael Peter da Emmanuel Shaibu bisa zargi mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya da kuma daukar doka a hannu.
- Dagaci ya rasa rawaninsa a Kano saboda badakalar filaye
- Zaben fid da gwanin PDP: Daliget 2 ne suka zabi Shehu Sani a Kaduna
Alkalin kotun, Mai Shari’a Cynthia Ikpe, ta ki amincewa da korafin masu kare kansu saboda rashin hurumi, kana ta ba da umarnin a tafi da su gdan gyaran hali na Makurdi ya zuwa lokacin da za a kammala binciken da ke kan gudana a kansu.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insfekta Friday Inedu, ya bayyana wa kotun cewa, wani mai suna Igoche Okopi da ke zaune a gida mai lamba biyar, Otia a yankin Ibamomaje cikin Karamar Hukumar Otukpo ta Jihar, ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na Otukpo a ranar 24 ga Afrilun 2022.
Inedu ya ce mai karar ya shaida musu cewa, jami’an tsaron sa-kai na Jihar Binuwai sun cafke wani dan uwansa da ke zaune a kauyen Otia a Otukpa bisa zargin satar babur.
Ya bayyana cewa, “A lokacin da jami’an tsaron suka yi kokarin kai wanda suka kama zuwa ofishinsu cikin motarsu kirar 406, sai wasu matasa suka bullo suka yi musu kawanya suka kwace shi.
“Sun lakada wa Omaga Okopi dukan tsiya da sanduna har da duwatsu, daga bisani suka kona shi kurmus,” inji shi.
Dan sanda mai shigar da karar ya ce, bayan samun labarin aukuwar lamarin, sun bi sawunsu inda a karshe suka cafke su.
Dan sandan ya ce sun kama Shaibu dauke da karamar bindiga kirar gida da kuma wata wuka.