✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗage taron mahaddata Qur’ani da za a yi a Abuja

Tun farko dai an saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron

Rahotanni sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu wanda za a gudanar a Abuja kamar yadda BBC Hausa ta bayyana.

An dai ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur’ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya.

Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, “tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro.

Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC dalilin da ya sa aka ɗage taron ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba.