✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci

Turkiyya ta ce bai wa ‘yan ta’addar PKK/YPG makamai ko ma da sunan mene ne, taimaka wa ta’addanci ne kai tsaye.

Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da Siriya ke ci gaba da fuskantar rashin kwanciyar hankali da kalubale masu yawa tun bayan kawo karshen mulkin Bashar al-Assad.

Manyan matsaloli sun haɗa da kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai daban-daban, rikice-rikicen filaye da ba a warware ba, tsoma bakin sojojin ƙasashen waje, da tattalin arziki mai rauni wanda ke fama da talauci da kuma ƙaura ta yawan jama’a.

Gwamnatin rikon kwarya ƙarƙashin jagorancin Ahmed al-Sharaa na fuskantar ƙalubale wajen neman sahihanci da amincewa, tare da barazana daga mabiyan Assad, ragowar mayakan ISIS, da hare-haren ‘yan tawayen.

Akwai kuma damuwa kan rawar da HTS ke takawa — kungiyar da ta jagoranci kifar da mulkin Assad — da kuma yiwuwar ta zama mai mulkin danniya.

Sai dai asu takardu na Ma’aikatar Tsaron Amurka sun kare kasafin kudinta na 2026, inda suka ce kudaden na da manufar horarwa, bayar da kayan aiki, da albashin wata-wata ga SDF da Mayakan Sa Kai na Syria dubu 19 da Amurka ke goya wa baya a Kudu maso Gabashin Syria, tare da wasu abokan aiki a Iraƙi da Lebanon.

Bayanan sun nuna cewa kayayyakin sun haɗa da ƙananan makamai tare da kayan kula da lafiya a kayan gyara, “kuma dawowar ‘yan ta’addar Daesh na barazana ga tsaron Amurka, jama’ar Iraƙi, Syria, Lebanon da ma jama’ar duniya baki ɗaya.’

YPG reshen PKK ne a Syria, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda, kuma kaso mafi tsoka da Pentagon ta ware a kasafin ya tafi ga ’yan tawayen PKK/YPG.

Daga cikin dala miliyan 130 da aka ware saboda Syria a kasafin kudin Pentagon na 2026, dala miliyan 7.42 za ta tafi ga Mayakan Sa Kai na Syria PKK/YPG, inda bayanan suka ce ana sa ran “kara karfinsu” wajen yaki da gyaran ‘yan ta’addar Daesh a Saharar Badiyah, sai dai kuma mafi yawan kudaden za su tafi ne ga ’yan tawayen SDF.

Kudaden baya-bayan nan na zuwa ne bayan an ba su dala miliyan 147.9 a 2025 da dala miliyan 156 a 2024, duk da sunan yaki da ‘yan ta’addar Daesh, matakin da Turkiyya ta nuna kin amincewa da shi saboda ana fakewa da hakan ana bai wa ‘yan ta’adda makamai a kan iyakarta.

A Ayyukan ta’addancin da ta ɗauki shekaru 40 tana yi, PKK, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda, ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da fararen hula, mata, da yara kanana.

Jaridar Kurdistan ta ruwaito Turkiyya nanata cewa bai wa ‘yan ta’addar PKK/YPG makamai ko ma da sunan mene ne, taimaka wa ta’addanci ne kai tsaye.