Wani babban kamfanin samar da magunguna na kasar Faransa, Sanofi, wanda yake aikin samar da rigakafin cutar coronavirus ya ce duk da cewa za a samar da shi ga kowa, Amurka ce za ta zama kan gaba wurin cin gajiyarsa.
A wata hira da ya yi da wani gidan talabijan a Amurka mai suna Bloomberg, shugaban kamfanin, Paul Hudson, ya ce kasar Amurka za ta fi kowa morar rigakafin idan aka samar da shi.
“Kasar Amurka za ta samu kaso mafi yawa daga rigakafin saboda ita ce ta dauki nauyin samar da shi”, inji Mista Hudson.
- Za a yi gwajin allurar riga-kafin coronavirus a Jamus
- ‘Tazargade ka iya yin tasiri wajen maganin coronavirus’
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa a watan Afrilu kamfanin na Sanofi ya hada gwiwa da kamfanin GlaxoSmithKline don samar da rigakafin coronavirus wanda ake sa ran za a kammala zuwa tsakiyar shekarar 2021.
Kamfanin na Sanofi ya sanar da cewa kwararrun ma’aikatansa suna aiki tukuru saboda gaggauta samar da rigakafin.
Ranar Laraba a shafinsa na Twitter kamfanin ya rawaito shugaban nasa yana cewa “Za a samar da rigakafin coronavirus ga kowa ba tare da nuna banbanci tsakanin kasashe ba”.