Amurka ta yi shelar tukwicin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayyana maboyar mutumin da ya kitsa harin Otel din Kenya na shekarar 2019 wanda ya kashe mutane fiye da 20 ciki har da Amurkawa da kuma jami’an tsaro.
Amurka ta bayyana sunan Mohamoud Abdi Aden a matsayin wanda ya kitsa harin na ranar 15 ga watan Janairun 2019 wanda kuma shi ne jagoran mayakan al-Shabaab a Somalia.
- Qatar na shirin sayen kungiyoyin Firimiyar Ingila uku
- Iran ta rataye tsohon jami’in gwamnatinta saboda zama dan leken asirin Birtaniya
Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan Amurkan ta sanya irin wannan tukwicin akan Maalim Ayman, shugaban al-Shabaab reshen Kenya.
Yanzu dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi shelar ladan dala miliyan 10 ga shugabannin kungiyar ta al- Shabaab biyar, wanda ya zarce duk wata kungiyar ta’addanci ta Sunni.
Amurka ta bayyana cewa Abdi Aden ya kitsa mabanbantan hare-haren da suka kashe tarin jama’a a kasashen da ke makwabtaka da Somalia.
Yayin harin na ranar 15 ga watan Janairun a shekaru 4 da suka gabata dai mayakan al-Shabaab sun yi wa Otel din DusitD2 da ke birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar kawanya, suka kuma shafe sa’o’i 20 suna kaddamar da hari tare da musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro a cikin Otel din.
Yayin harin dai wanda ya kashe mutane 21 ciki har da wasu Amurkawa, jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka dukkanin maharan.
Jakadar Amurka a Nairobi Meg Whitman ta shaida wa manema labarai a birnin Nairobi cewa a shirye suke su biya dala miliyan 10 ga duk wanda ya gano maboyar dan ta’addan.