✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta kashe ‘mai shirya wa IS hari’ a Afghanistan

Amurka ta ce akwai yiwuwar IS ta sake kai hari filin jirgin sama da ke Kabul.

Amurka ta ce ta kashe ‘mai shirya’ wa kungiyar IS reshen kasar Afghanistan (ISIS-K) hare-hare a wani harin da jiragenta marasa matuka suka kai ranar Asabar.

Amurka, ta kai harin saman ne a matsayin ramuwar gayya ga harin kunar bakin wake da ISIS-K ta kai filin jirgin sama na birin  Kabul, inda  hukumomin lafiya suka ce mutum kimanin 170 sun mutu.

Wani hafsan sojin Amurka, Kaftin Bill Urban, ya ce mutumin da jiragen suka kashe da dare ranar Asabar babban jigo ne na kungiyar IS, kuma akwai yiwuwar daukar karin matakin a kan kungiyar a nan gaba.

“Alamu na farko sun nuna cewa mun kashe wanda aka kai wa hari,” a lardin Nangarhar da ke Gabashin Kabul da ke iyaka da kasar Pakistan, a cewar jami’in na Babbar Cibiyar Tsaron Amurka.

Harin da IS ta kai filin jirgin Kabul ya kashe ’yan Afghanistan sama da 150 da kuma jami’an Amurka 13, kuma shi ne hari mafi muni da aka kai wa sojojin Amurka cikin shekara goma a Afghanista.

Harin ya tilasta wa dakarun Amurka yin hadin gwiwa da Taliban domin lura da aikin kwashe mutanen Afghanistan da ke son barin kasarsu ta filin jirgin na Kabul.

Shugaba Joe Biden ya yi alkawari a ranar Alhamis cewa Washington za ta dauki mataki a kan wadanda suka aikata laifin.

A yayin da take kokarin kammala kwashe dakarunta da fararen hula daga Afghanistan, Amurka ta ce akwai babban hadarin kungiyar za ta ci gaba da kai hare-hare a filin jirgin.

– Yiwuwar sabon hari

Jami’an Amurka sun ce sake kai harin a tashar jirgin saman Kabul abu ne da kusan babu makawa, akwai kuma yiwuwar zai iya yin barna fiye da harin ranar Alhamis.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Kabul ya gargadi Amurkawa da su kaurace wa filin jirgin sama sannan ya ce wadanda ke kofar su gaggauta janyewa.

– Ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan

Bayan shafe shekara 20 a Afghanistan, dakarun Amurka da na kasahen NATO suna rigerigen kammala kwashe mutane da ficewa daga Afghanistan kafin cikar wa’adin ranar Talata da Shugaba Joe Biden ya sanya.

Amurka da kawayenta sun fitar da kimanin mutum 111,900 daga Afghanistan a cikin makonni biyu da suka gabata, inji ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya zuwa ranar Asabar, sojojin Amurka da ke filin jirgi na Kabul ba su kai 4,000 ba, idan aka kwatanta da soja 5,800 a lokacin da ake kan ganiyar aikin kwashe mutanen.

– Abin da Taliban ta ce

Harin kunar bakin waken ISIS-K na ranar Alhamis ya lakume rayuka da dama a wajen kofar tashar jirgin saman, inda dubban ’yan Afghanistan suka taru don kokarin barin kasar a jirgi bayan Taliban ta karbe ikon Kabul a ranar 15 ga watna Agusta, 2021.

Masu magana da yawun kungiyar Taliban da ke iko a Afganistan yayin da sojojin Amurka suka janye, ba su yi karin bayani kan harin da jiragen suka kai ba.

’Yan Taliban makiyan kungiyar IS ne kuma sun ce sun cafke wasu da ake zargi da hannu a harin filin jirgin saman na ranar Alhamis.

Fadar White House ta ce mai yiwuwa a ’yan kwanaki masu zuwa su kasance mafi hatsarin aikin kwashe mutane a Afghanistan.