Sojojin Amurka sun hallakaDakarun Amurka sun hallaka jagoran kungiyar ISIS a yankin Gabas ta Tsakiya da Turai Abd-al-Hadi Mahmud al-Haji Ali, da wasu mataimakansa biyu a kasar Syria.
Ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon), ta ce Abd-al-Hadi Mahmud al-Haji Ali shi ne kwamandan IS da ke tsare hare-haren da kungiyar take kaiwa a Yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Turai.
- ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a hanyar kasuwa a Binuwai
- Yau INEC za ta yi taron gaggawa kan Zaben Adamawa
Hedikwtar tsaron (CENTCOM) ta ce, Abd-al-Hadi Mahmud al-Haji Ali “Shi ne hadafin harin,” da aka kai da helikwafta bayan ta gano shirinsa na yin garkuwa da wasu jami’ai a kasashen waje domin biyan bukatun kungiyar.
Sanarwar, wadda kakakin CENTCOM, Kanar Colonel Joe Buccino ya fitar ta ce ko da yake kashe Abd-al-Hadi zai raunana IS a yankin Gabas ta Tsaya, amma an kashe maciji ne ba a sare kansa ba.
A safiyar Litinin ne CENTCOM ta sanar cewa ta kashe wasu mutum biyu masu dauke da makami, amma harin bai taba fararen hula ba.
Kakakin kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Obseratory, Rami Abdel Rahman, ya ce mutum uku aka kashe a harin, kuma biyu daga cikinsu an kashe su ne a kauyen Jarabulus, gabas da birnin Aleppo, kafin wayewar garin Litinin.
Tun a shekarar 2015 Amruka ta girke dakarunta a Syria domin taimaka wa mayakan Kurdawa wajen yakar kungiyar IS.