✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta jefa wa Falasɗinawa tallafin abinci daga jiragen sama

Jiragen saman sun jefa ƙullin abinci 38,000 a wani wuri a Zirin Gaza.

A karon farko Gwamnatin Amurka ta jefa wa Falasɗinawa tallafin abinci ga al’ummar Gaza ta jiragen sama.

Aƙalla  ƙulli 38,000 na abinci jiragen saman Amurka uku suka jefa wa al’ummar Gaza a Yammacin wannan Asabar ɗin.

Falasɗinawa sun riƙa yada bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna ƙunshin akwatunan kayan abincin da jiragen yaƙin Amurka na C-130 ke jefo musu.

An gudanar da aikin rabon abincin tare da haɗin gwiwar sojojin saman Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta bayyana.

Jami’an Amurka sun ce abincin da aka rabar shi ne na farko daga cikin da yawa da shugaba Joe Biden ya bayyana ranar Juma’a.

Shugaba Biden ya alƙawarta kai agajin abinci zuwa Gaza, bayan da aka kashe sama da mutum 100 da ke dakon jiran agajin abincin tallafi a ranar Alhamis

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce jiragen saman sun jefa ƙullin abinci 38,000 a wani wuri a Zirin Gaza

A baya wasu kasashe irin su Birtaniya da Faransa da Masar da Jordan sun taba jefa wa al’ummar Gaza tallafin abinci ta sama, to sai dai wannan shi ne karon farko da Amurka ta yi hakan.