Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da dakatar da wasu shirye-shirye da su kunshi ba da agaji ga Nijar bayan hambarar da zababben shugaban kasar da majalisar soji ta yi.
A karshen makon da ya gabata ne Faransa ta dakatar da duk wani taimakon raya kasa da take bai wa Nijar bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.
- Yanzu da nake shugabanci ne ya fi dacewa Kwankwaso ya dawo APC – Ganduje
- ‘Barayi’ sun kone shaguna 20 bayan yin sata a tsohuwar kasuwar Gombe
Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashe da dama ma sun dakatar da goyon bayansu.
Duk da haka, “za a ci gaba da taimakon agajin jin kai na ceton rai da abinci” kuma Amurka za ta ci gaba da gudanar da ayyukan diflomasiyya da tsaro don kare jami’anta a kasar, in ji shi.
Nijar na samun kusan dala biliyan biyu a duk shekara a matsayin taimakon raya kasa a hukumance, a cewar Bankin Duniya.