✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta bukaci China ta daina azabtar da Musulmin kabilar Uighur

Yadda kasar China ke kamawa tana garkame al’ummar Musulmi ’yan kabilar Uighur da sauran tsirarin Musulmi a wasu sansanoni da ke kasar, ya ja hankalin…

Yadda kasar China ke kamawa tana garkame al’ummar Musulmi ’yan kabilar Uighur da sauran tsirarin Musulmi a wasu sansanoni da ke kasar, ya ja hankalin Amurka, wadda ta yi tir da hakan, tare da kiran China ta daina.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya bayyana cewa yadda ake kamawa tare da garkame al’ummar Musulmin wadanda akasari ’yan kabilar Uighur ne da sauran tsirarun al’ummomi Musulmi da kasar China ta yi a wasu sansanonin da ke yankin Dinjiang na yammacin kasar, abin akwai takaici da tayar da hankali, sannan ya ce Amurka na yin Allah wadai da wannan aika-aika.

“Mun sha fitowa fili muna yin tir da haka, kuma mun yi ta tattaunawa da China a kebance kan wannan batu,” inji Pompeo, yayin da yake amsa tambayar da Muryar Amurka ta yi masa kan batun.

Ya kara da cewa Amurka na iya bakin kokarinta don ganin ta shawo kan China ta gane cewa hakan bai dace ba, kuma ta daina.

Dama kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ma sun zargi kasar ta China da garkame miliyoyin ’yan kabilar Uighur.

A martaninta, China ta ce shirin kawar da tsaurin ra’ayi take yi, kuma ana koyar da ayyukan yi da doka da kuma harshen Sin na Mandarin a sansanonin.