Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce Amurka ce tushen yakin da ake gwabzawa a halin yanzu tsakanin Ukraine da Rasha.
Khamenei ya fadi hakan ne a cikin wani jawabi da ya yi a talabijin inda ya tabo batun yakin Rasha a Ukraine.
- ASUU: An tashi baran-baran a tattaunawar Ministan Ilimi da shugabannin dalibai
- Burkina Faso ta amince da mulkin soji na shekara uku
A cikin jawabinsa ya ce “Ukraine ta fada tarkon manufofin rikici na Amurka.
“Muna goyon bayan kawo karshen yaki a Ukraine, amma maganin ko wane rikici shi ne a gano tushensa.
“Amurka ce tushen rikici a Ukraine,” in ji Khamenei.
Ya ce “Amurka na kirkirar yaki ne a sassan duniya domin neman kasuwar makamanta.”
BBC ya ruwaito cewa duk da ya shafe tsawon minti daya yana magana kan rikici amma Ayatollah bai ambaci Rasha ba, wadda dakarunta suka afka Ukraine.
Ya kara da cewa Amurka ba abin yarda ba ce – ra’ayin da ake gani cikas ne ga tattaunawar nukiliya da Iran ke yi da manyan kasashen duniya kan farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.